Alfijr ta rawaito Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, yana taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da na kasashen waje murnar halartan bikin na bana a ranar Litinin 10 October 2022.
Ya kuma shawarci dukkan ‘yan Nijeriya da su yi koyi da halin soyayya, hakuri, juriya da wadanda su ne kyawawan dabi’u na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya misalta,
Ya kuma kara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro da a kasar nan.
Alfijr ta rawaito
Aregbesola ya bukaci ‘yan Najeriya musamman musulmi da su guji tashe-tashen hankula da rashin bin doka da oda da sauran ayyukan ta’addanci.
Yayin da yake kira da a dakatar da duk wani hali na raba kan al’umma a fadin kasar nan, Ministan ya bukaci daukacin ‘yan Nijeriya, musamman matasa, da su rungumi kyawawan dabi’u na aiki tukuru da zaman lafiya ga ’yan Adam, ba tare da la’akari da imani, akida, zamantakewa da kabilanci ba.
Ya kara da cewa hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinta na gina kasa mai kishin kasa wanda dukkan ‘yan kasa za su yi alfahari da ita.
Alfijr Labarai
Ministan ya yi wa daukacin musulmi fatan murnar zagayowar wannan rana, sannan kuma ‘yan Nijeriya za su yi biki.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller