Wannan na kunshe ne cikin wata tattaunawa da Kwamishinan yaɗa labarai da ayyukan cikin gida Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyanawa yan jarida a safiyar Alhamis, biyo bayan zaman da majalisar Zartaswa na 26, ta gabatar a zamanta na ranar Laraba.
Waiya ya ce wadannan kuɗaɗen zasu tafi ne a bangaren lafiya, ilmi, gine gine da ayyukan tituna tare da mugudanan ruwa da ababen more rayuwa a fadin jihar Kano, wanda majalisar ta sahalewa Gwamna Abba Kabir domin a fara ayyukan cikin gaggawa.
Wasu daga cikin muhimman ayyukan da za a yi shine dawo da wasu makarantun kwana na yan mata 13, da waccen gwamnatin ta rufe su, saboda rashin kishin ilmin mata a jihar Kano duk da irin tarihin da makarantun suke da shi da kuma gudanarwar da suke bayar wajen yaye fitattun mata a jihar. In ji Waiya.
Hakazalika gwamna Abba ya amince da fidda makudan kuɗaɗe wajen gyara kasuwar Farm Centre da kara fadadata domin samun cigaban matasa da maganin zaman banza a jihar, duk da kasuwar bata gwamnati bace.
Wannan tattaunawar an gabatar da ita ne a dakin taro na ma’aikatar Yaɗa Labarai da harkokin cikin gida tare da manya manyan kwamishinini guda 4, da mashawarta Na mai girma Gwamna.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD