Iyaye mata da yan mata ne suka fito zanga-zangar suna kira a kawo karshen fadan daban dake haddasa asarar rayukan yayansu babu gaira babu dalili.
Yanzu haka dai tuni jami’an tsaro suka isa wajan domin kwantar da tarzoma.
Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da alummar unguwar ke alhinin rasa rayukan wasu da ake zargin yan daba da kashewa sakamokon fadan dabar da ya barke a jiya Juma’a.
Masana da dama na dora alhakin wanzuwar fadan daba tsakanin matasa sakamokon rashin aikin yi da kuma karancin ilimi.
Wannan lamari na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin Kano ta gabatar da sabbin jami’an da zasu dakile masu sana’ar kwacen waya da kuma fadan daba a fadin jihar.



Hikima Radio
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t