Masu Aikin Hako Yashi Su Biyar 5, Sun Mutu Nan Take A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar da suka makale a karkashin tulin yashi a kauyen Yanlami dake karamar hukumar Bichi.

Alfijr

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kano, ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Asabar.

“Mun samu kira daga tashar kashe gobara ta Bichi cewa ramin tafkin ya rufe mutane biyar.

Mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:05 na safe,” inji Abdullahi.

Alfijr

Ya bayyana sunayen wadanda abin ya shafa da Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 da Jafaru Abdulwahabu mai shekaru 30 da Jibrin Musa mai shekaru 30 da Masaudu Nasiru mai shekaru 25 da Muhammad Sulaiman mai shekaru 35. domin su taimaki abokinsu da zai aura ya gina gida.

Wani bangare na yashi ya rufta ya rufe su kuma suka mutu daga baya,”

Alfijr

Abdullahi ya ce a cikin sanarwar. Ya ce an mika gawarwakin zuwa ga ‘yan sanda da hakimin kauyen Yanlami.