Kwamishinan da ya tsayawa dilan ƙwaya aka bada belinsa a kotu a Kano ya magantu

FB IMG 1753453958041

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya baiyana cewa ba shi da alaƙa ta kusa ko ta nesa da Sulaiman Danwawu, shahararren dillalin miyagun ƙwayoyin Nan na jihar.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Namadi ya tsaya wa Danwawu aka bada belinsa yayin da ya ke fuskantar shari’a a kotun tarayya da ke Kano kan zargin laifuka da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Kwamishinan ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da wanda ake zargin a matsayin shahararren ɗan safarar ƙwayoyi.

A cewarsa, ya amince ya tsaya masa ne kawai bayan wasu mutane amintattu sun tabbatar masa da cewa wanda ake zargin ba shi da wata mummunar ɗabi’a.

Yayin da ya bayyana cewa kotu ce a raɗin kanta ta bada belin wanda ake zargi, Namadi ya ƙara da cewa tsayawa beli ga wanda ke fuskantar shari’a ba saɓawa dokokin ƙasa ba ne.

“Saboda haka, yana da muhimmanci a fayyace cewa shiga cikin wannan lamari ba ya da nasaba da wata alaƙar sirri ko kusanci da wanda ake zargi, amma na yi ne da kyakkyawar niyya.

“A bayanin alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a M.S. Shuaibu, a cikin hikimarsa, ya bayar da beli ga wanda ake zargi bayan sauraron roƙon lauyoyinsa a ranar 17 ga Yuli. Yana da muhimmanci a jaddada cewa bayar da beli a irin waɗannan lokuta wani sahihin tsarin shari’a ne, domin wanda ake zargi ana ɗaukar sa a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa.

“Haka kuma, la’akari da cewa wani ɓangare na sharuddan beli ya buƙaci wanda zai tsaya masa daga cikin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, wasu mutane amintattu gare ni suka zo suka roƙe ni da in taimaka. Sun ba ni tabbaci a kan sa, kuma na amince da hakan cikin gaskiya da yarda.”

“Ni har ga Allah ban san girman laifin da ake tuhumar sa da shi ba, ko kuma irin rikicin da ya ƙunsa ba. Na tsaya masa ne bisa yarda da wasu amintattun mutane da su ka roƙe ni na yi hakane,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “abubuwan da aka bankado game da wanda ake zargin sun matuƙar girgiza ni,” in ji Namadi.

Ya kuma yaba da yadda gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ke kokaein yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *