Daga Aminu Bala Madobi
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Aminu Gidado Yusha’u a matsayin babban mai kula da ayyukan raya kasa na Kano, Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACRESAL).
ACRESAL wani shiri ne na Bankin Duniya tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Jihohin Arewa 19, ciki har da Birnin Tarayya Abuja.
Rahotonni sunceta nadin nasa ya biyo bayan daga darajar Kodinetan Ayyukan na baya, Dr. Dahir M. Hashim, da Gwamna Yusuf ya yi zuwa kwamishina kuma mamba a majalisar zartaswar jihar a farkon wannan shekarar.
A cikin sakon taya murna da sa hannun kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano Dakta Dahir M. Hashim a ranar Talata ya bayyana nadin Aminu Gidado Yusha’u a matsayin wanda ya cancanta.
‘’Nadin da akayi maka bai zo da mamaki ba, idan aka yi la’akari da sadaukarwar da ka yi na aiki tuƙuru. Ina da cikakken kwarin gwiwa game da kwarewar ka na aiwatar da aikin da aka ba ka, da tallafa wa hangen nesa na Mai Girma, da kuma tafiyar da aikin wajen cimma muhimman manufofinsa, in ji sanarwar.
”Ina fatan za ka zage damtse don baiwa mara da kunya a wannan muhimmin matsayi”
Har zuwa lokacin da aka nada Aminu Gidado Yusha’u shi ne jami’in sa ido da tantancewa na shirin ACRESAL na Kano.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t