An kama Danbilki Bisa Zargin Bata Sunan Gwamna Kan Bada Cin Hanci

Alfijr

Alfijr ta rawaito wata kotu a Kano ta tura keyar Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan zuwa 15 ga watan Maris.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne a gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.

Alfijr

Ana tuhumar Kwamanda ne da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.