Ɓullar Baƙin Halittu A Katsina Shifcin Gizo Ne — Ƴansanda

Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta ƙaryata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda wasu baƙin halittu su ka mamaye Katsina.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Gambo Isah ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a jiya Litinin a Katsina.

“An jawo hankalin rundunar ƴan sandan kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda wasu baƙin halittu suka mamaye Katsina.

Don haka hukumar tana so ta bayyana ƙarara cewa abubuwan da ke cikin bidiyon gaba daya na bogi ne.

“Wannan wani yunkuri ne na kawo naƙasu ga zaman lafiya da mutanen jihar ke samu ta hanyar wani mummunan hali,” in ji Mista Isah, mai muƙamin Sufeto.

Katsina video

Don haka kakakin ya bukaci jama’a da kada su firgita, su yi watsi da faifan bidiyon a matsayin shirin gizo ne kawai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *