Boka Ya Ragargaje Kayan Bokancin Sa Tare Da Musulunta

Daga Aminu Bala Madobi.

Alfijr ta rawaito wani boka a kasar Burkina Faso Mai suna Sékou Traoré ya yi kaca kaca da kayan bokancin sa tareda rungumar addininin musulunci.

Rahotanni sun nuna cewa, bokan yace ya kwashe tsawon lokaci yana bugun kasa tare da kulla harkoki da iskokai da aljanu.

Bokan, Sekou Traoré yace daga karshe ne ya ga uwar bari tare da gane gaskiya Inda ya lalata dukkan kayan bokancin nasa sama da 631.

Kafofin labaran cikin gida a Burkina Faso sunyi tsinke a gidan shahararren bokan, inda dandazon mutane sukai cikar kwari domin ganewa idanun su wannan al’amari.

Daganan bokan yace yayi da nasani shigar sa harkar bokanci tare da kira masu aikata irin wannan alamari da su daina domin ba wani haske a harkar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *