Alfijr ta rawaito Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceci rayuka 45 da dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 285.6 a cikin gobara 86 da ta afku a watan Maris, kamar yadda kakakinta, Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana a ranar Litinin.

Ya kara da cewa, mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da gobarar ta lalata dukiyoyin da ta kai Naira miliyan 113.2 a lamarin.
Sanarwar ta ce hukumar ta amsa kiran ceto 43 da kuma na karya guda 10 daga mazauna jihar cikin wannan lokacin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ