Zanga-zanga: An hayo ƴan daba don su tada fitina da sunan kwankwasiyya a Kano — In Ji Gwamna Yusuf

FB IMG 1719671782992

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zargin cewa wasu masu adawa da gwamnatin sa sun ɗauko hayar ƴan daba domin su tada fitina a jihar a yayin zanga-zangar da ake shirin farawa gobe Alhamis.

Alfijir labarai ta ruwaito gwamna Yusuf ya yi wannan zargi ne a yayin wata ganawa sarakuna, malamai da yan kasuwa a gidan gwamnati a yau Laraba.

A cewa gwamnan, gwamnatin sa ta samu sahihan bayanan sirri cewa wasu ƴan siyasa marasa kishin jihar Kano sun yo hayar ƴan daba, har daga wajen Kano domin su tada fitina a jihar.

Ya ce “manufar su iya ce su yi amfani da zanga-zangar da za a fara gobe sai su tada fitina a jihar kuma in sha Allah, Allah ba zai basu nasara ba.

“An siyo jajayen huluna za a raba musu domin su farwa al’umma da dukiyoyin su da sunan cewa yan Kwankwasiyya ne su ka yi.

“To mu mun san wannan ba dabi’a ce ta ƴan Kwankwasiyya ba. Saboda haka mu na kira ga jami’an tsaro cewa duk wanda aka kama yana wannan ta’ada a kama shi a hukunta shi,” in ji Gwamnan.

Gwamna Yusuf ya ce zai yi iya kokarin sa na ganin an gudanar da zanga-zanga cikin lumana, inda ya kara da cewa gwamnatin sa a shirye take da ta gana da shugabannin zanga-zangar domin shawo kan lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *