Gwamna Abba Kabir Yusuf ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta rage farashin man fetur da kudin wutar lantarki.
Alfijir labarai ta ruwaito Gwamnan ya yi rikon ne a ranar Laraba yayin ganawa da Malamai da Sarakuna da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a yayin da ake shirin fara zanga-zanga.
A cewar Gwamnan, tsadar man fetur da karin kudin wutar lantarki ya haifar da damuwa ga ‘yan Najeriya wanda hakan yasa suke shirin fita zanga-zanga.
“Yakamata gwamnati ta duba karin kudin wuta da aka yi. Wani karin matsala ne ga ‘yan Najeriya. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta rage farashin wanda hakan zai saukakawa ‘yan Najeriya”, inji shi.
Game da zanga zangar kuma, Gwamna Abba ya bayyana cewa duk da cewa doka ta bada damar a yin zanga-zanga amma dole ne ta zama ta lumana.
Sannan ya ce bazai je ko ina ba, zai tsaya ya tarbi masu zanga zangar tare da mika kokensu ga shugaban ƙasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj