Wutar Rikici Ta Kunnu Tsakanin Ladin Cima (Tambaya) Da Nazir Adam A Kannywood

Alfijr

Alfijir ta rawaito Ladin Cima matar malam Mamman (Tambaya) ta ce, tunda na fara film ban taɓa yin Film ɗin da aka ban dubu 50 ba, wani lokacin ma dubu 2 ake bani! Inji ta

Alfijr

fitacciyar Jaruma mai fitowa a matsayin uwa a shirye shiryen Kannywood mai suna Ladin Cima Haruna, ta bayyana cewa ba’a biyan ta kudi masu yawa idan aka ɗauke ta Film.

Ta bayyana haka ne a wata tattaunawa da tayi BBC Hausa, cikin shirin daga bakin mai ita.

Alfijr

Ladin Cima, ta bayyana yadda ta fara harkar Film da kuma irin nasarorin da ta samu, a lokacin da aka tambaye ta ko ta taɓa samun ƙalubale a harkar Film.

Ta bayyana cewa tunda na baro NTA Kaduna zuwa NTA Kano ban taɓa cin karo da wata matsala ba sai a bana, matsalar da ba kowa na iya gayawa ba sai daga baya.

Alfijr

A cewar ta saura ƙiris ta koma kwana a Kasuwar Bata dake Kano, saboda rashin muhallin zama, tace lokacin da na gama aikin Gwamnati, ta nemi na fita daga gidan da nake ciki domin na Gwamnati ne, to bayan na fita ne na shiga matsala.

An sake tambayarta cewa, tsawon shekaru da kika kwashe kina harkar Film bakiyi tanadin wani abu bane.

Alfijr

Ta bayyana cewa, tun da na fara film, kawo yanzu, ban yi film ɗin da aka ɗauki dubu hamsin ko dubu talatin ko dubu ashirin aka ba ni ba, balle in yi tanadin wani abu.

Ta ƙara da cewa, idan na fita Film sai dai a bani dubu biyar, ko dubu huɗu, ko dubu 3, a cewar ta ko yau ɗin nan da ka ganni naje wani wajan ɗaukar wani Film amma wallahi dubu biyu aka bani.

A cewar ta a ƙalla ina ciyar da yara bakwai to ya za ayi dubu biyu tai min wani abu bare, har na siyi gida.

Alfijr

Fitaccen marubuci a masana’antar Kannywood, Nazir Adam Salihi, wanda aka fi sani da dan Hajiya ya karyata batun da jaruma Ladin Cima ta yi cewa ba a taba biyan ta kudi masu kauri kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook ranar Alhamis kamar yadda Aminiya ta tuntubi shi ta wayar tarho.

Da yake bayani, fitaccen marubicin ya ce, na biya Ladi Cima (Tambaya) N40,000 a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta N30,000 a kashi na hudu.

Alfijr

“Haka nan ko wata daya ba a yi ba na sake biyan ta N30,000 a wani dan bidiyo na fadakarwa kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba.

“Haka nan mun yi gyaran scene guda wanda magana kawai ta yi muka biya ta N5,000 muka kuma saya mata abinci na kusan N4,000 a wuni guda.

Alfijr

Dan Hajiya ya sake cewa a gabana, Hadiza Gabon ta ba ta N270,000 kyauta! Amma duk da haka ka ji halin dan Adam. Kai jama’a!”