Wasu mutane wadanda ba a san ko su waye ba sun farfasa motar da tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa Muhammad, take amfani da ita wajen zuwa asibiti domin ci gaba da jinyar ta, lamarin da ya jawo alhini da Allah-wadai daga masu tausaya mata.
Lamarin ya faru ne da rana a ranar Alhamis da ta gabata bayan an kai motar wajen wankewa. Bayan an gama wanke ta, an ajiye ta domin ta bushe kafın wasu da ake zargin batagari suka isa wurin, suka farfasa motar sannan suka tsere ba tare da an gano su ba.
An ce Halisa ba ta samu labarin abin da ya faru ba sai bayan wani lokaci, lokacin da aka sanar da ita irin barnar da aka yi wa motar.
Da aka tuntube ta kan ko akwai wanda take zargi da aikata wannan ta’asa, sai tsohuwar jarumar ta ce bata zargin kowa.
“Gaskiya ba na zargin kowa. Amma rayuwa ce, wasu suna yi maka fatan alheri, wasu kuma suna jin haushin ka, ba tare da wani dalili ba,” inji ta.
Halisa ta bayyana cewa motar ba tata ba ce, an ba ta ne aro saboda halin rashin lafıyar da take ciki.
Ta ce: “Mai motar tana zaune ne a Abuja. Da ta ga irin wahalar da nake sha wajen zuwa asibiti, sai ta ba ni aron motar domin in rika amfani da ita. Amma abin takaici wasu suka zo suka farfasa ta ba tare da wani dalili ba.”
Jaruma Halisa Muhammad ta dade tana fama da cutar sankarar mama, inda ta shafe tsawon lokaci tana neman magani a ciki da wajen Nijeriya. A tsawon wannan lokaci ta fuskanci kalubale iri-iri, ciki har da zargin damfara da ya shafi kudaden tallafın da aka tara domin kula da lafıyar ta.
A baya, Gwamnatin Jihar Kano ta ba ta tallafın naira miliyan bakwai domin taimaka mata wajen jinya. Sai dai wani mutum da aka damka wa kudin domin shirya tafiyar ta zuwa Saudiyya ya gaza cika alkawari, inda aka ce ya mayar da naira miliyan biyu kacal, yayin da har yanzu ake neman ya dawo da sauran naira miliyan biyar.
Majiyoyi sun ce fitaccen jarumi Ali Nuhu ma ya taba shiga tsakani domin a samu warware matsalar, sai dai har yanzu ba a samu nasara ba.
A wani sako da ta wallafa bayan fasa mata mota, Halisa ta bayyana cewa duk da abin da ya faru, ta mika lamarin ta ga Allah.
Ta ce, “Muna gode wa Allah a kowane hali. Allah ya isar mana! Muna rokon Allah ya bayyana gaskiya, ya dawo mana da hakkin mu, ya kare mu daga sharrin miyagu.”
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t