Majalisar zartarwar Najeriya ta aminince da yiwa NYSC gyare-gyare da canje-canje

FB IMG 1782766556819

Majalisar Zartarwa ta tarayyar Najeriya (FEC) karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da yin gyare-gyare ga tsarin yi wa kasa hidima (NYSC).

Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Ya ce gyaran zai kunshi cikakken nazari da sake duba tsarin shirin na NYSC domin ya dace da bukatun zamani.

An kafa shirin NYSC a shekarar 1973 bayan yakin basasar Najeriya da nufin karfafa hadin kai da zumunci tsakanin matasa masu digiri daga sassa daban-daban na kasar.

Tsawon shekaru 53 da kafuwar shirin, NYSC ta taimaka wajen hada kan matasa da kuma inganta hadin kan kasa.

Sai dai ministan ya ce sauye-sauyen da suka faru a kasar cikin shekaru da dama sun sa ya zama dole a sake fasalin shirin, yana mai cewa bukatun Najeriya sun canza, kuma ana sa ran manufofin NYSC su ma su dace da sabon yanayin da ake ciki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *