Sunan Muhammad ya ci gaba da kasancewa sunan da aka fi sanya wa jarirai maza da aka haifa a Ingila da Wales cikin shekaru uku a jere, bayan kusan yara maza 6,000 sun samu sunan a shekarar 2025.
Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Birtaniya (ONS) ta fitar sun nuna cewa sunan Noah ne ya zo na biyu, inda tazarar da ke tsakaninsa da Muhammad ta karu zuwa kusan jarirai 2,000. Tun daga shekarar 2023 ne sunayen Muhammad da Noah ke rike da matsayi na farko da na biyu.
A jerin sunayen yara maza, Leo da Luca sun hau matsayi na uku da na hudu, inda suka wuce Arthur, Oliver da George.
ONS na kirga bambancin rubutun sunaye daban-daban, inda baya ga Muhammad da ya zo na farko, Mohammed ya zo na 20, yayin da Mohammad ya kasance na 55. Idan aka hada su, sama da jarirai maza 2,600 sun samu wadannan nau’ikan rubutun sunan.
A bangaren jarirai mata kuwa, Olivia ta ci gaba da zama sunan da aka fi sanyawa, sai Lily, Amelia, Isla da Florence.
Rahoton ya nuna cewa sunan Muhammad na kara samun karbuwa a tsawon shekaru, inda ya shiga cikin sunaye 100 mafi shahara tun a 1997, sannan ya shiga cikin manyan sunaye 10 tun a 2016. Haka kuma, nau’in rubutun Mohammed ya fara shiga cikin jerin sunaye 100 mafi shahara a Ingila da Wales tun shekarar 1924.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t