Alfijir Labarai Media Service
Kotun Tsaure dake karamar hukumar Shanono yadda ta lalace na rantse da girman Allah da a ajiye mutum a cikinta gwanda a kai mutum gidan Gyaran Hali saboda masifar ragargajewa da kazanta! Haka kotun Zarewa dake karamar Rogo ita ma abin sai imani.
Wani bincike na musamman da Alfijir Labarai Media Service ta gudanar a wasu Kotunan Shari’a da ke faɗin Jihar Kano ya bankado yadda wasu daga cikin kotunan ke fuskantar matsananciyar lalacewar gine-gine da kayayyakin aiki. Binciken ya nuna cewa akwai kotuna da ke aiki cikin yanayi da bai dace da muhimmancin wuraren da ake gudanar da adalci ba.
A yayin zagayen binciken, an tarar da rufin kwano na wasu kotuna na zub da ruwa, bangon gine-gine sun tsage, wasu rufin na dab da ruftowa, tagogi sun lalace, yayin da kayan daki da sauran kayayyakin aiki suka tsufa tukuf sakamakon shekaru da dama ba tare da gyara ba. Rahoton ya ce irin wannan yanayi na haifar da ƙalubale ga Alƙalai, ma’aikatan kotuna, lauyoyi da masu neman shari’a.
Binciken ya nuna cewa duk da jajircewar Alƙalai da ma’aikatan shari’a keyi wajen gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da gaskiya, yanayin gine-ginen wasu kotunan na iya rage karsashi da kwarin gwiwar masu amfani da su tare da shafar yadda jama’a ke kallon tsarin shari’a.
Daga cikin kotunan da abin yafi tsamari akwai Babbar Kotun Shari’a ta garin Gani da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila da kuma Babbar Kotun Shari’a ta Madobi, waɗanda rahotanni suka nuna suna buƙatar kulawa da gyare-gyare domin inganta yanayin gudanar da shari’a a kotunan.
Sai dai rahoton ya yaba da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta riga ta ware kuɗaɗe a kasafin kuɗi domin gyaran wasu Kotunan Shari’a, ciki har da na Kofar Kudu da Yankaba, tare da shirin sake gina Kotun Shari’a ta Mekalwa da kuma gina ƙarin kotuna a sassan jihar.
Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga gwamnati da ta hanzarta aiwatar da waɗannan ayyuka tare da faɗaɗa su zuwa sauran kotunan da ke yankunan karkara, domin tabbatar da cewa dukkan al’umma suna samun damar gudanar da shari’a cikin muhalli mai tsafta, tsaro da mutunci.
Rahoton ya kammala da cewa inganta Kotunan Shari’a ba gyaran gine-gine kaɗai ba ne, wata hanya ce ta ƙarfafa adalci, kare martabar tsarin shari’a da kuma ƙara amincewa a zukatan jama’a.
Tabbas lalacewar wasu Kotunan Shari’ar a Jihar Kano ta kai wani mataki da ya kamata ya tayar wa kowa hankali. Wasu daga cikin gine-ginen sun tsufa matuƙa, bangwaye sun tsage, rufuffuka na zub da ruwa, wasu sassa da kayayyakin kotunan tamkar tsumma da aka yar a gefe bayan an gama amfani d ita. Wannan yanayi bai dace da wuraren da ake yanke hukuncin adalci ba.
Abin takaici shi ne, duk da irin jajircewar Alƙalai da ma’aikatan kotuna wajen gudanar da aikinsu, suna yin hakan ne a cikin muhalli mara martaba da ingancin da ya kamata. Kotun shari’a ita ce fuskar adalci, kuma idan gine-ginenta suka lalace haka, hakan na iya rage kwarin gwiwar masu neman hakkinsu da kuma amincewar al’umma ga tsarin shari’a.
Yayin da Gwamnatin Jihar Kano ke ci gaba da zuba jari a fannoni daban-daban na ci gaba, lokaci ya yi da za a bai wa Kotunan Shari’ar Musulunci kulawar da ta dace. Gyaran waɗannan kotuna ba wai kawata gine-gine ba ne kawai, mataki ne na kare martabar adalci da tabbatar da cewa wuraren da ake yanke hukunci suna nuna daraja, mutunci da kimar tsarin shari’a kafin matsalar ta ƙara muni.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t