NDLEA ta kama wata ƴar ƙasar Afirka ta Kudu da hodar iblis a filin jirgin sama na Abuja

FB IMG 1783875566137

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wata ƴar ƙasar Afirka ta Kudu mai shekara 38, Will Jessica Ann, a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bisa zargin shigo da kilogram 5.75 na hodar iblis (heroin) zuwa Najeriya.

A cewar NDLEA, an kama matar ne a ranar 6 ga Yulin 2026 bayan ta iso daga Doha na ƙasar Qatar tare da ɗanta mai shekara uku.

Hukumar ta ce ta ɓoye ƙwayoyin a cikin akwatuna biyu, kuma da farko ta musanta mallakarsu kafin daga bisani ta amsa cewa nata ne.

NDLEA ta kuma ce bincike ya nuna matar na da alaƙa da wata ƙungiyar fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa da ke aiki tsakanin Cambodia da Afirka ta Kudu.

A wani samame daban a filin jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, jami’an NDLEA sun kama wani direban babur mai suna Onyechere Chinadu da ya dawo daga Madagascar ɗauke da kilogram 1.715 na methamphetamine.

Haka kuma, hukumar ta ce ta kama buhuna 8,287 na tabar wiwi ta zamani (Canadian Loud) masu nauyin kilogram 4,143.5 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, waɗanda darajarsu ta haura Naira biliyan 10.3.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar kan nasarorin da suka samu tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *