Maniyyatan Jihar Kano za su biya kuɗin ajiye kujerar aikin Hajjin 2027 cikin wa’adin watanni biyu da rabi, daga 12 ga Yuli zuwa 26 ga Satumba, 2026, kamar yadda Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar.
Shugaban Hukumar, Alhaji Ibrahim Matawalle, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a Kano.
Ya ce an kayyade kuɗin kafin alkalamin kujerar Hajjin 2027 kan Naira miliyan takwas (₦8,000,000) ga kowane maniyyaci, tare da ƙarfafa masu niyyar zuwa aikin Hajji da su kammala biyansu cikin wa’adin da aka tanada.
Matawalle ya kuma bayyana cewa dukkan kuɗaɗen za a biya ne ta hanyar bank draft, wanda za a miƙa wa jami’an cibiyoyin Hajji na ƙananan hukumomi domin kammala rajista.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
