Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yadda ta samu a bara.
Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji ta Nijeriya, ta sanar da ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026.
Exploring Ba Vi’s Dragon Fruit Garden [NếmTV]
NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar.
’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti
Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an ƙayyade ƙafin alƙalamin kuɗin kujerar domin fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.
Hajiya Fatima ta ambato shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana cewa an ƙayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alƙalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.
Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yadda ta samu a bara.
Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Nijeriya.
A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t