Mazauna yankunan Yandodo, Mai-Allo, Oromi, Mariri, Yargana da Tsamiya Babba da ke ƙananan hukumomin Nassarawa, Kumbotso da Gezawa a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta cigab da aikin titin Yandodo–Mai-Allo–Oromi–Mariri, suna zargin cewa jinkirin aiwatar da aikin na ci gaba da jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali.
Rahotanni na nuni da cewa duk da gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar aikin tun a watan Oktoban shekarar 2025 tare da kafa allon aikin a wurin, har yanzu ba a fara cikakken aikin ginin titin ba. Sun ce lalacewar hanyar, wadda ta cika da manyan ramuka da zaizayar ƙasa tare da yawaitar ambaliya a lokacin damina, na hana zirga-zirga cikin sauƙi tare da jefa rayukan mata masu juna biyu da marasa lafiya cikin haɗari.
Direban adaidaita sahu, Adamu Alhassan, ya shaida wa Global Tracker cewa mata masu juna biyu huɗu sun haihu a cikin babur ɗinsa a lokuta daban-daban saboda rashin yiwuwar isa asibiti cikin lokaci sakamakon munin hanyar.
A cewarsa, idan naƙuda ta tsananta yayin tafiya, yakan tsaya a wani wuri mai aminci domin ba matar kariya har sai ta haihu kafin ya garzaya da ita da jaririn zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Shi ma Shugaban Direbobin Adaidaita Sahu na yankin, Hussaini Sa’idu, ya ce matsalar hanyar ta ƙara tsananta wahalhalun da al’umma ke fuskanta, musamman mata masu juna biyu, yara da tsofaffi. Ya ce idan aka yi ruwan sama mai ƙarfi, ambaliya kan mamaye hanyar na sa’o’i, lamarin da ke katse zirga-zirga tare da hana jama’a isa kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya.
Mazauna yankin sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki domin tabbatar da komawar kamfanin da aka bai wa kwangilar zuwa bakin aiki ba tare da wani ƙarin jinkiri ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga hukumomin gwamnati ko kamfanin da ke gudanar da aikin kan dalilin jinkirin ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t