Hukumar Alhazan Kano ta bayyana dalilan da ya sa har yanzu ba su sanar da kudin aikin Hajjin 2027 ba

IMG 221650 08726 1783545423515

Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu ba ta sanar da kudin na gani ina so aikin Hajjin 2027 ba saboda ana ci gaba da kammala tsare-tsare da su ka dace.

Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa Matawalle, ya ce za a sanar da kudin ajiyar da zarar an kammala dukkan tsare-tsaren da suka shafi aikin Hajjin 2027.

Ya ce a aikin Hajjin 2026, hukumar ta yi jigilar dukkan alhazan Kano 3,611 zuwa Saudiyya tare da dawo da su Najeriya cikin koshin lafiya, ba tare da an bar ko da mutum guda a can ba.

Matawalle ya bayyana cewa hadin gwiwar da aka yi da Hukumar NAHCON, kamfanonin jiragen sama da hukumomin Saudiyya ya taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin cikin nasara.

Ya kuma ce hukumar ta gano tare da kwaso kusan jakunkuna 30 da aka bari a masaukan alhazai, da sama da jakunkuna 100 da aka bari a filayen jiragen saman Saudiyya, inda aka dauki matakin dawo da su Kano domin mika su ga masu su.

Darakta Janar din ya yabawa alhazan Kano bisa ladabi da biyayyarsu yayin gudanar da aikin Hajjin, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta yi amfani da darussan da ta koya wajen inganta shirye-shiryen aikin Hajji na gaba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *