Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar da zai baiwa gwamnatin jihar damar kafa sabbin hukumomi biyu domin kula da harkokin tsara da bunƙasa birane, tare da soke dokar da ta kafa Hukumar Tsarawa da Bunƙasa Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).
Sabon ƙudirin dokar, mai suna Dokar Tsare-tsaren Muhalli da Kula da Bunƙasa Gine-gine ta Jihar Kano, ya tsallake karatu na uku a zaman Majalisar da aka gudanar ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore. Africans & Diaspora
Da yake yiwa manema labarai bayani bayan kammala zaman, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Hon. Lawan Hussaini Dala, ya ce amincewar da Majalisar ta yi da sabon ƙudirin doka ta kawo ƙarshen dokar da ta kafa KNUPDA, domin bai wa gwamnati damar sake fasalin tsarin kula da ci gaban birane a jihar.
Ya bayyana cewa, bisa tanadin sabuwar dokar, gwamnatin jihar za ta kafa Kano Metropolitan Development Authority (KAMDA), wadda za ta kula da harkokin bunƙasa birane da tsara gine-gine a cikin babban birnin Kano, da kuma Kano Area Development Control Authority (KADKA), wadda za ta riƙa kula da irin waɗannan ayyuka a sauran sassan jihar. Demographics
A cewarsa, hukumomin biyu za su karɓi dukkan ayyuka da alhakin da KNUPDA ke gudanarwa a baya, tare da aiki ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Muhalli ta Jihar Kano.
Hon. Dala ya ƙara da cewa, kafa sabbin hukumomin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin inganta tsarin tsara birane, tabbatar da bin ƙa’idojin gine-gine, dakile take dokokin muhalli, da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin Jihar Kano.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
