Majalisar Dattijai Ta Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Dubi Allah Su Dubi Annabi Su kara bawa Tinubu Lokaci

FB IMG 1722442104786

Majalisar dattawa ta bukaci masu shirya zanga-zangar a fadin kasar da su dakatar da shirye-shiryensu su kara bawa Gwamanti lokaci domin warware matsalolin ƙasar

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi wannan roko ne bayan wani zaman gaggawa da Sanatocin suka yi a Abuja A Yau Laraba.

Kamar yadda KBC News ta ruwaito, kungiyoyi daban-daban na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agusta domin magance tsadar kayayyaki da fatara da yunwa a kasar.

Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, wacce ta shafe shekara guda a kan karagar mulki, tuni ta bullo da tsare-tsare da za su amfani ‘yan Nijeriya nan gaba kadan. Ya kuma bukaci a yi hakuri, inda ya bayyana cewa, shirin da aka yi kwanan nan, kamar rattaba hannu kan dokar mafi karancin albashi na kasa, kafa hukumar raya shiyyar Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas, da baiwa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, matakai ne na rage yunwa da fatara.

“Majalisar dattawa ta bukaci masu zanga-zangar da su kara baiwa gwamnati lokaci,” in ji Akpabio.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *