Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukunci a ranar Laraba cewa rushewar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi wa wata katafariyar cibiya mallakin Tiamin Multi Services Global Limited a unguwar Gyadi-Gyadi bata bisa ka’ida.
Mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad Karaye ya bayyana cewa gwamnati ta saba dokar ƙasa wajen kwace filin tare da rushe gine-ginen ba tare da sanarwa ko ba wa kamfanin damar kare kansa ba.
“Kwace filin ba tare da sanarwa ba ya sabawa kundin tsarin mulki da dokar Land Use Act,” in ji mai shari’a Karaye.
Kamfanin ya bayyana cewa gine-ginen da aka rusa sun kasance na asibitin zamani da ake ginawa a Court Road, Gyadi-Gyadi, da ke ƙaramar hukumar Tarauni kafin gwamnati ta kwace filin a shekarar 2021.
Kotun ta tabbatar da cewa takardun mallakar filin – LKN/COM/2017/116 (LPKN 1188), MLKN01622 da MLKN01837 – har yanzu na da inganci kuma suna nan daram.
Kotun ta bayyana kwace filin da rushe ginin yayin da karar ke gaban kotu a matsayin raini ga dokokin ƙasa da rashin mutunta tsarin shari’a.
Kotun ta ba da umarnin a biya kamfanin Tiamin Multi Services diyyar Naira biliyan 2 da miliyan 125 a matsayin diyya na musamman kan tsaikon ci gaba, sannan kuma a biya wata Naira miliyan 500 a matsayin diyyar hasarar gama gari da aka jawowa kamfanin sai kuma Naira miliyan goma diyyar kudaden da aka kashe a bangaren shari’a
Haka kuma, kotun ta ba da umarnin cewa gwamnati ta gaggauta ficewa daga filin kuma ta dakatar da duk wani yunƙuri na ci gaba da hana mallakar filin ga kamfanin
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD