Daga A’isha Salisu Ishaq
Babbar Kotun Majistare me lamba 24 dake Zamanta a Harabar Filin saukar Jiragen Sama na Aminu Kano ta aike da wasu Matasa su biyu zuwa Gidan gyaran hali.
Matasan biyu, Umar Tijjani Mazaunin Unguwar Dorayi Karama (Unguwar Bello Da kuma Usman Isa Usman (Wanda aka fi kira da Bawan Allah) Mazaunin Unguwar Jaen, Layin Dagaci, an gurfanar dasu ne bisa laifi tuhume tuhume guda hudu, Hada kai don aikata laifi, Haura Gida, Sata da kuma yin barna. Bayan da aka karanto musu tuhume tuhumen da ake yi musu dukkanin su sun amsa Laifuffukan.
Daga nan ne Mai gabatar da Kara Lauyan Gwamnati M. Bello ya roki Kotun data hukunta su, bisa wannan laifin da suka aikata.
Mai Shari’a Muttaka Abba Dandago ya dage zartas da hukunci zuwa ranar 29 ga Watan Yuli, 2025 kuma ya bayar da umarnin tisa keyar su zuwa Gidan gyaran hali har zuwa ranar da za’a dawo Kotun.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan π
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ