Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya hannu kan wata doka, da ta yi wa dokar kasafin kudin 2025 kwaskwarima, inda aka rage kwatankwacin kusan kashi tara da rabi cikin 100 na kasafin kuɗin da aka amince da shi a watan Disamban da ya gabata.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a hukumance daga ofishin babban sakataren gwamnatin ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa wasu abubuwa ne suka janyo zaftare wani kaso daga cikin kasafin kuɗi na shekara ta 2025.
“An zaftare kasafin kuɗin daga CFA biliyan dubu uku zuwa CFA biliyan dubu 2,749,” in ji sanarwar.
Wani masani kan fannin tattalin arziki a ƙasar, Mohaman Chiroma ya ce gwamnatin ta yi haka ne saboda ta hango cewa ba za ta iya samun kuɗaɗen da take hankoron samu ba.
Wannan dai na cikin alkawura da aka yi da asusun ba da lamuni na duniya IMF a lokacin wani bita da aka yi, in ji sanarwar da sakataren gwamnatin ƙasar ya fitar.
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD