Kotu ta tsare wani shugaban makaranta da malaminsa kan zargin lalata da ɗaliba

FB IMG 1760790928482

Kotun Majistare mai lamba 16, da ke Gombe ta bayar da umarnin tsare shugaban makarantar Destiny Treasure International School, Nasiru Barau Manu, da wani malamin makarantar, Eleazer Yila, a gidan gyaran hali kan zargin lalata da wata ɗaliba mai shekara shida.

Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa ana zargin Eleazer Yila da aikata laifin a watan Yulin 2026 a harabar makarantar da ke unguwar Arawa a birnin Gombe, lamarin da ya tonu bayan yarinyar ta sanar da mahaifiyarta abin da ya faru.

Haka kuma, ana zargin shugaban makarantar da ƙoƙarin yi wa lamarin rufa-rufa da kare malamin maimakon ya kai hukumomin da suka dace rahoto.

Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen da suka shafi lalata da kuma ɓoye wanda ake zargi da aikata laifi, duka waɗanda ake tuhuma sun amsa laifin.

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barrista Manir Mohammed Sambo, tare da Barrista Nafi’u Abubakar da ke sa ido kan shari’ar, sun shaida wa kotun cewa laifukan sun saɓa da tanade-tanaden Sashe na 285 da na 167 na Dokar Penal Code.

Alƙaliyar kotun, Babbar Majistare Hamaira Bema Demba, ta amince da buƙatar masu gabatar da ƙara na gudanar da taƙaitacciyar shari’a.

Kotu ta kuma bayar da umarnin tsare waɗanda ake tuhumar a gidan gyaran hali, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuli, 2026, domin yanke hukunci.

Trust Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *