Jami’an tsaro sun kama Adeniyi Adeyemi wanda ake zargi da kirkirar hukumar bogi

IMG 182653 14726 1784050033955

Bayan umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja, tuni jami’an tsaro su ka kama Darakta Janar na hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Adeniyi Adeyemi, bayan ya gaza halartar zaman shari’ar da ake yi masa kan zargin amfani da jabun takardu.

Mai shari’a Muhammed Umar ya bayar da umarnin ne bayan lauyan Adeyemi ya bayyana cewa ya kasa shawo kan wanda yake karewa ya halarci kotun.

Lauyan gwamnati ya ce an dage shari’ar sau da dama bisa bukatar Adeyemi, amma ya ci gaba da kin zuwa kotu duk da cewa ya taba bayyana sau daya kacal tun bayan shigar da karar.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026.

A baya dai Fadar Shugaban Kasa ta musanta wanzuwar PFIPC, tana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta kafa irin wannan hukuma ba, kuma ba ta nada Adeyemi a matsayin jami’inta.

Sai dai Adeyemi ya musanta wannan ikirari, inda ya yi zargin cewa wasu jami’an gwamnati sun karbi kudade domin tabbatar da nadinsa. A martanin da Fadar Shugaban Kasa ta fitar, ta ce Adeyemi na fuskantar tuhume-tuhume takwas da suka hada da amfani da takardun bogi, bayan da ‘yan sanda suka ce sun gano takardun jabun nada da hatiman gwamnati a ofishinsa da gidansa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan πŸ‘‡

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *