Kotu ta sanya 15 ga wata don fara shari’ar da Faisal ya shigar da gwamnatin Kano kan rushe masa gidaje guda 10

FB IMG 1723959647845

Babbar kotun jiha mai lamba 13 wadda ta ke zaman ta a Miller road karkashin jagorancin Mai shari’a  Zuwaira Yusif ta sanya ranar 15 ga watan da muke ciki dan sauraron wata kara wadda wani mutum mai Suna Faisal Abdulmunaf ya shigar yana karar gwamnatin jihar Kano akan batun rushe masa gidaje guda goma, biyar daga ciki sunkai matakin hawa na biyu, biyar kuma suna matakin farko we wato foundation.

Gidajen suna kan titin Mukhtar Muhammed link daura da babban titin Ahmadu Bello Way.

Mai karar ta bakin lauyan sa ya bayyana wa kotun cewar wadanda ake kara sun rushe masa gidajen duk da cewar ya cika duk wata ka’ida ta mallakar filayen tare da cika dokokin ma’aikatar hukumar lura da filaye da tsara birane.

Mai korafin ya gabatar da wasu takardun mallaka da satifiket mai lamba LKN/COM/2002/485/LKN/2002/487. Wadda ke kunshe da filaye daga na daya zuwa na goma.

Cikin kunshin takaddun karar shafi na biyu sadara ta 4. da ta 5 da ta 6 mai karar ya roki kotun da ta sanya gwamnatin jihar Kano ta biya shi Naira Biliyan uku da miliyan dari shida da tamanin da bakwai da dubu dari takwas da tara da dari takwas da ashirin da takwas da kobo sittin da bakwai a matsayin ramko.

Sai kuma Naira Biliyan daya da ya roki a biya shi sakamon tashin hankalin da ya ce ya hadu da shi.

Mai karar ya kuma nemi a biya shi Naira miliyan dari biyu kudin a matsayin kudin haya mafi kankanta da yakamata ya samu duk shekara akan wadannan gidajen guda Goma.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnati da na mai kara sun tafka muhawara akan suka da lauyoyin gwamnati suka yi.

An kuma roki kotun da ta hana gwamnatin jiha ko wasu wakilanta daga yin tasarifi da wajen da ake magana akansa. kotun ta sanya ranar 15 ga watan nan da muke ciki dan sauraron kowane bangare domin cigaba da shari’a da bayyana matsayar ta akan wannan danbaruwa.

Rahma TV

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *