Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta sallami manyan jami’an ‘yan sanda hudu daga aiki, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa kan wasu jami’ai 31 bisa laifuffuka daban-daban da suka shafi rashin ɗa’a da ƙwarewar aiki.
An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar hukumar da aka gudanar a hedikwatarta da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Ladabi da Hulɗa da Jama’a na PSC, Torty Njoku Kalu, ya sanya wa hannu, hukumar ta bayyana cewa jami’an huɗun da aka sallama an same su da laifukan munanan halaye, rashin ƙwarewar aiki da kuma aikata abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’ar jami’an gwamnati.
Hukumar ta kuma amince da ɗaukar matakan ladabtarwa kan wasu manyan jami’an ‘yan sanda.
Daga cikin matakan da aka ɗauka, an rage wa jami’ai 10 matsayi, inda aka mayar da Sufetandan ‘Yan Sanda (SP) guda uku zuwa Mataimakin Sufetan ‘Yan Sanda (DSP).
Haka kuma, an rage wa Mataimakan Sufetan ‘Yan Sanda guda biyu matsayi zuwa Mataimakin Sufetan ‘Yan Sanda na Farko (ASP), yayin da aka mayar da ASP guda biyar zuwa matsayin Sufeto (Inspector).
Bugu da ƙari, an tilasta wa jami’ai biyu yin ritaya saboda abin da hukumar ta bayyana a matsayin maslahar jama’a.
Sauran hukuncin sun haɗa da bai wa jami’ai 10 tsawatarwa mai tsanani, jami’ai biyar kuma aka yi musu tsawatarwa ta yau da kullum.
An kuma bai wa jami’ai uku wasiƙun gargaɗi, yayin da jami’i guda ya samu wasiƙar shawara. Sai dai jami’ai bakwai da ake zargi sun tsira daga zarge-zargen bayan bincike ya wanke su daga duk wani laifi.
Da yake jawabi, Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), Hashimu Salihu Argungu, ya sake jaddada aniyar hukumar na tabbatar da ɗa’a a cikin Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya (NPF).
Ya ce hukumar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin ɗa’a daga jami’an ‘yan sanda ba.
A cewarsa: “Kwamitin gudanarwar PSC na yanzu ƙarƙashin jagorancina ba zai amince da kowace irin rashin ɗa’a daga jami’an ‘yan sanda ba. Za mu ci gaba da tabbatar da ɗa’a tare da yabawa da ba wa lada ga jami’an da suka nuna ƙwarewa, jajircewa da kwarewar aiki.”
Hukumar ta bayyana cewa waɗannan matakan ladabtarwa sun nuna ƙudirin ta na ƙarfafa ɗaukar alhaki, ƙwarewar aiki da kuma ƙara amincewar jama’a ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.
Sawaba
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t