Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1447.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar Kano da su yi addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasa tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama (S.A.W) ya koyar.
Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD