Gwamnan ya umarci sabon kwamishinan da ya gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da rikon amana tare da tabbatar da kyakkyawan zaton da ake dashi a kansa.
Kwamishinan Sharia Barr. Haruna Isa Dederi ne ya jagoranci rantsuwar yayin zaman majalisar zartaswar karo na 28 wanda ya gudana a sabon gidan gwamnati dake rukunin gidajen Kwankwasiyya.
Wannan na zuwa ne bayan da a baya tsohon kwamishinan ma’aikatar Major General Muhammad Inuwa Idris mai ritaya ya ajiye mukaminsa a matsayin kwamishinan Ma’aikatar bisa radin kansa, inda kuma nan take gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da aje mukamin nasa.
Ma’aikatar tsaron cikin gida wata sabuwar ma’aikata ce da gwamnati mai ci karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta kirkirota domin inganta tsaro a jihar Kano.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD