Tun da fari dai an gurfanar da harira Muhammad Tudun Murtala a babbar kotun shari’ar musulunci dake zamanta a First office karkashin jagorancin Munzali Tanko Soron Ɗinki, bisa zargin aure cikin aure, zalika aka gurfanar da wani matashi mai suna Bello Abubakar ‘Yankaba.
Da yake yanke hukuncin Alƙalin kotun ya hori harira Muhammad Tudun Murtala ta haddace hizifi goma da ga Alkur’ani mai girma a wata makarantar islamiyya a unguwar ta Tudun Murtala.
Zalika Alƙalin ya hori harira ta biya mijin data aura na biyu sadakinsa naira dubu 100.
Sai dai a nasa bangaren mijin matar na biyu mai suna Bello Abubakar Ƴankaba ya ce, ya yafe mata wannan kuɗi.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD