Gwamnan Kano ya aika da sunan sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa zuwa Majalisar dokoki

IMG 20250426 WA0030

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya turawa Majalisar dokokin jihar sunan Sa’idu Yahya domin tantance shi don nada shi a matsayin shugaban hukumar Karbar korafe-korafe da Hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano .

Hakan ya biyo bayan wa’adin aikin tsohon Shugaba hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya Cika , inda bayan ya sauka aka nada Zaharadden Hamisu Kofar mata a matsayin shugaban hukumar na rikon kwarya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya turawa manema labarai.

Bature ya ce Sa’idu Yahya Ƙwararre ne kuma masani a Kan harkar yaki da cin hanci da rashawa, inda yayin aiki a hukumar dake yaki da rashawa ta ICPC .

Ya ce ya rike mukamai da dama kuma ya na da Kwarewa Sosai ta yadda zai yaki cin hanci da rashawa .

Sanarwar ta ce Wanda aka baiwa mukamin Rikon kwaryar Wato Zaharadden Hamisu Kofar Mata an mayar da shi ma’aikatar Harkokin shari’a ta jihar Kano.

Gwamnan ya yabawa Muhuyi bisa yadda ya Jagoranci hukumar da kuma gudunmawar da ya bayar wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano .

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *