Gwamnatin Katsina ta magantu kan masu tsegunta wa Yan bindiga bayanai don kai hare-haren jihar

IMG 115023 01825 1754045437847

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga bayanai ne ke haddasa kashi 80 cikin 100 na hare-haren yan bindiga a faɗin jihar.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a jihar.

Mu’azu ya ce masu kwarmata wa ƴan bindigar bayanai da ke kai musu abinci da sauran abubuwa ne ke ba su bayanan da suke buƙata domin ƙaddamar da hare-hare.

Kwamishinan ya ce hakan kuma na matuƙar kawo wa gwamnati tsaiko wajen yaƙi da matsalar ƴan fashin daji a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin irin waɗannan mutane kan kai wa ƴan bindigar abubuwan da suke buƙata har dazuka su kuma sayar musu a farashi mai tsada.

“A ɗaya daga cikin waɗannan garuruwa an taɓa kama wani mutum na sayar da kwalbar lemo naira 3,000 ga ƴan bindiga, wani kuma na sayar musu man fetur kan naira 5,000 kowace lita”, kamar yadda ya bayyana.

“Haka ma akwai masu kai miyagun ƙwayoyi su sayar musu a farashi mai yawa, sun mayar da hakan sana’ar da suke samun kuɗi masu yawa”, in ji shi.

Kwamishinan ya yi zargin cewa wasu ma daga ciki kan haɗa baki da ƴan bindigar wajen sace mutanen da suke so a sace ciki kuwa har da danginsu.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *