Gwamna Abba Kabir ya rattaba hannu kan kasafin kudi na 2023, kusan Biliyan 59

FB IMG 1697237741177

“Wannan karin kasafin kudin an yi shi ne domin a kula da ci gaban ababen more rayuwa na shekarar 2023, domin biyan bukatun al’ummar jihar Kano.”

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kasafin kudin na shekarar 2023 wanda ya kai biliyan hamsin da takwas, miliyan dari da casa’in da daya, da dubu dari biyar da talatin da biyar, naira goma sha takwas, kobo goma sha biyu (N58, 191, 535, 018.12).

Yayin da yake gabatar da kasafin kudin, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta bi ka’idojin kula da kasafin kudi domin kudaden da aka ware za su yi amfani da su cikin gaskiya da adalci.

“Wannan karin kasafin kudin an yi shi ne domin a kula da ci gaban ababen more rayuwa na shekarar 2023, domin biyan bukatun al’ummar jihar Kano.” Gwamnan ya bayyana.

Gwamnan ya yaba da kokarin kwamishina, tsare-tsare da kasafin kudi na gaggawar aiwatar da takardar kasafin kudin ga majalisar jiha.

Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Jibrin Ismail Falgore wanda ya jagoranci manyan hafsoshi na majalisar kwamitin rabon kudaden ne ya gabatar da kudirin amincewar gwamnan a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamnan ya kuma bukaci a ci gaba da samun goyon baya da kyakyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dokoki a jihar Kano.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya sanyawa hannu a ranar juma a

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

One Reply to “Gwamna Abba Kabir ya rattaba hannu kan kasafin kudi na 2023, kusan Biliyan 59”

  1. Allah yasa suyi amfani dashi ta hanyar da ta dace,a kula da ILIMI da LAFIYA,DAN WLH HARKAR ILIMI da LAFIYA,YA KARA TABARBAREWA a JAHAR KANO,zama mu’iya cewa gwara gwomnatin baya ma,Muna Kira ga wakilan mu su kula da yanayin ILIMI yake da LAFIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *