Ƴan sanda sun kama yan ta’adda da makamai a cikin wasu motoci 10 yayin wani sintiri a Abuja

Screenshot 20231006 133605 com.facebook.katana edit 3114434061501

Sabbin motocin da rundunar ‘yan sandan ta kirkiro ‘Anti-One Chance Squad’ ne suka damke motocin domin dakile duk wata barazana da ke faruwa a babban birnin tarayya Abuja.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta kama wasu motoci 10 da ake zargin an yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Haruna Garba, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce sabbin motocin da rundunar ‘yan sandan ta kirkiro ‘Anti-One Chance Squad’ ne suka damke motocin domin dakile duk wata barazana da ke faruwa a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, akasarin motocin da aka kama suna dauke da bakaken gilashi, (Tinted) kuma a yayin bincike an gano gatari, da wukake, da ake ganin ana amfani da su wajen gudanar da ayyukansu na aikata laifuka daga cikin motocin.

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen uku da aka kama da motocin.

Mista Garba ya ce jami’an rundunar ‘yan sanda reshen Zuba, a ranar 8 ga watan Oktoba, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan wani kiraye-kirayen da aka yi musu kan shakkun wasu mutane a kusa da kasuwar ‘ya’yan itace ta Zuba.

“Jami’an ‘yan sanda daga sashin Zuba sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kama wani da ake zargin, wanda da ganin jami’an ‘yan sandan, sai ya ranta a na kare.

An kai ruwa rana da shi, in da daga bisani jami’an ‘yan sanda suka kama shi.

“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi daya ne daga cikin wasu ƴan ta’adda da ake musu lakabi da ƴan biyar, sannan ya jagoranci ‘yan sanda suka kama wasu ‘yan kungiyarsa guda biyu,” inji shi.

A cewar CP, ‘yan sandan sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu, mujallu biyu da harsashi 35 daga gidan wadanda ake zargin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *