Jami’an Bijilante sun kama wani mutum mai suna Bauhari da ake zargi da satar allunan Maƙabartar Unguwa Uku dake karamar Hukumar Tarauni Jihar Kano
Alfijir labarai ta ruwaito lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na dare yayin da Jami’an Bijilante suke gudanar da aikin su gefan makabartar dake kusa da ofishin INEC dake unguwar.
Wanda ake zargi “ya ce sana’ar sa itace gwan-gwan, Dan haka ya kan je makabarta dan gudanar da sace allunan alamomi na kaburbura.
Rahotanni na nuni da cewa Al,umma na zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe allunan alamomi na kaburbura.
Sai dai wasu masu sana’ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.
Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewar wannan kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka akicinsu.
A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu dan wata mummunar manufa.
Adamu Abubakar Fiya Fiya Zonal Kwamandan Rundunar Bijilante dake Unguwa uku a zantawarmu da shi ya ce, rundunar ta samu nasarar cafke mutumin da ake zargin mai suna Bauhari.
Fiya Fiya ya ce bayan samun rahoton satar allunan maƙabarta a baya yasa suke tsaurara Tsaron maƙabartar.
Ya kara da cewar bayan kammala Bincike zamu turasa wajan jami’an ƴan sanda domin fadada binciken.
Jaridar Inda Ranka
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
