Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce mutum takwas sun nutse a ruwa sannan wasu 13 sun mutu a cikin gidajen da mamakon ruwan ya rushe su.
Alfijir labarai ta ruwaito shekarar 2022 kusan mutum 195 ne suka mutu kuma lamarin ya shafi mutum 400,000, waɗanda da yawansu suka rasa gidajensu.
Mamakon ruwan sama da amabaliyar da aka shafe tsawon mako uku ana yi a Nijar sun yi sanadin mutuwar mutum 21, lamarin da ya shafi kusan mutum 6,000, a cewar alkaluman Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a ranar Alhamis.
Ma’aikatar ta ce mutum takwas sun nutse a ruwa sannan wasu 13 sun mutu a cikin gidajen da mamakon ruwan ya rushe su.
Wasu mutum 26 din sun jikkata sannan kusan dabbobi 4,000 sun mutu ko sun ɓata, a cewar jami’ai a jawabin da suka yi a gidan talabijin na ƙasar.
Tun shiga daminar bana yankin Maradin ne mummunan yanayin ambaliyar ya fi shafa, inda jami’ai suka ce mutum 14 ne suka rasu a can.
Yawanci dai a kan fara damina ne daga watan Yuni har Satumba a ƙasar ta Yammacin Afirka.
A shekarar 2022 kusan mutum 195 ne suka mutu kuma lamarin ya shafi mutum 400,000, waɗanda da yawansu suka rasa gidajensu.
AFP
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj