Da Dumi Duminsa: Hisbah Ta Haramta Sana’ar Tura Fina-finai Ta Waya (Downloads) a Faɗin Jihar Kano Baki Ɗaya

FB IMG 1784155223444

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana’ar tura fina-finai ta wayar salula, wato downloads, a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar. Sanarwar ta fito ne ta bakin Mukaddashin Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Dr. Mujahid Aminuddeen, wanda ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumar ke yi na kare tarbiyyar al’umma, ɗabi’u nagari da kuma tabbatar da bin koyarwar addinin Musulunci.

Sheikh Dr. Mujahid Aminuddeen ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna yadda wannan sana’a ke taimakawa wajen yaɗa fina-finai da bidiyoyi masu ɗauke da abubuwan da suka saɓa wa addini, al’ada da kyawawan ɗabi’u. Ya ce saboda haka ne hukumar ta yanke shawarar dakatar da wannan sana’a domin kare matasa daga gurɓacewar tarbiyya da kuma rage yaɗuwar abubuwan da ke haddasa lalacewar zamantakewa.

Mukaddashin Babban Kwamandan ya gargaɗi masu gudanar da sana’ar da su gaggauta dakatar da ita, yana mai cewa hukumar za ta ɗauki matakan doka kan duk wanda aka kama yana ci gaba da gudanar da aikin bayan wannan sanarwa. Haka kuma ya yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma da matasa da su mara wa Hisbah baya wajen tabbatar da nasarar wannan mataki, yana jaddada cewa manufar hukumar ita ce kare addini, tarbiyya da zaman lafiyar al’ummar Jihar Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *