Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu masu girma shuwagabanninmu
Cikin girmamawa da takaici tare da bakin ciki nake sanar daku irin asarar rayuka da raunuka tare da dukiyoyin al’umma da ake rasawa a kullum ta Allah a hanyar garin ƙarfi zuwa garin Kura sakamakon aikin titin da ake mutane kuma suke bin hannu daya!
Mai girma shugaban Kasar Najeriya Bola Tinubu da mai girma gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf tsawon wata uku ko sama da haka wannan masifar take faruwa a wannan titin, wanda a kullum ta Allah ba a mutu ba, mutum 5 ko sama da haka sai sun rasa rayukansu, kusan mutane 50, kuma sai sun jikkata, ban da asarar dukiya.
Ganin wannan masifar ta yi yawa Jaridar Alfijir Labarai ta ga dacewar tunatar da ku kamar yadda kuka saba laya yayin kama aiki kan zaku kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da kuke mulka!
Alhaji Hamza na ɗaya daga cikin mazauna garin Kura ya bayyana mana cewar, babu wata rana da za’a wayi gari da ba’ayi hatsari a wannan hanya ba.
Tun ana iya kokarin magance matsalar amma abun yaci tura, Kuma ga dukkan alamun lamarin yafi karfin jami’an dake kula da kiyaye haddura na FRSC dana Karota masu taimawa a hanyar.
Hamza ya kara da cewar Kullum asibitin garin na Kura sai ya karbi mutanen da suka samu raunuka da Kuma gwarwakin al’umar da suka rasa rayukansu a dalilin wannan hanyar!
A don haka ne al’umar yankin ke kira ga shugaban ƙasar Najeriya da gwamnan Kano dasu dubi girman Allah da Manzonsa su dauki matakin gaggawa domin ceto rayukan al’uma da sauran matafiya dake bin wannan hanyar.
Da fatan wannan sakon zai isa ga wajen wadanda abin ya shafa ko zasu yi saurin daukar matakin gaggawa ameen summa ameen.





Mai muku fatan alheri
Musa Best Seller D/iya
Editan Jaridar Alfijir Labarai
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t