Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ƙara bai wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) tallafi, ciki har da samar da ƙarin motocin aiki, domin ƙarfafa yaƙi da safara da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a saƙon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Faruq Ibrahim, ya gabatar yayin bikin ƙona fiye da tan 12 na miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace bayan kotu ta ba da umarnin lalata su.
An gudanar da bikin ne a yankin Kalebawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.
Gwamnan ya ce yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana buƙatar haɗin kan al’umma domin dakile matsalar da ke barazana ga rayuwar matasa da zaman lafiyar jama’a.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da fito da sabbin tsare-tsare da shirye-shirye da za su taimaka wajen rage yawaitar safara da amfani da miyagun ƙwayoyi.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NDLEA na Ƙasa, Janar Muhammad Buba Marwa (mai ritaya), wanda Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar (DCG) Ahmad Sulaiman Ningi ya wakilta, ya yi kira ga gwamnatin jiha, ƙananan hukumomi, hukumomin tsaro da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ci gaba da haɗa kai da NDLEA wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi.
Shi ma Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Dahiru Lawan Yahaya, ya bayyana cewa tabar wiwi ce ta fi rinjaye a cikin miyagun ƙwayoyin da aka lalata, tare da wasu nau’ikan ƙwayoyi da aka ƙwace daga hannun masu laifi.
Ya ƙara da cewa ana gudanar da lalata miyagun ƙwayoyin ne a bainar jama’a ne kawai bayan samun sahalewar kotu, domin tabbatar da gaskiya da bin doka.
Bikin ƙona miyagun ƙwayoyin ya samu halartar kwamandojin NDLEA daga jihohin maƙwabta, shugabannin hukumomin tsaro, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki masu goyon bayan yaƙi da safara da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.





Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t