Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3 Ta Kuma Lalata Gidaje 1,453 A Jihar Bauchi

Alfijr ta babban Daraktan Hukumar kare Muhalli ta Jihar Bauchi, BASEPA, Ibrahim Kabir ya tabbatar da mutuwar mutane 3 sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje 1,453 da gonaki da dama a Kananan Hukumomin Zaki da Gamawa.

Alfijr Labarai

Daraktan ya bayyana haka ne a lokacin da yake shaida wa Gwamna Bala Mohammed, a wata ziyarar jajantawa al’ummar da abin ya shafa a jiya Asabar, a Ƙaramar Hukumar Zaki.

Ya ce bayan tantance irin ɓarnar da mamakon ruwan sama ya yi a ranar Laraba, an gano ya kashe mutane 3 da lalata gidaje 1,453 da gonakin da ba a tantance adadinsu ba a kananan hukumomin biyu na jahar.

Kabir ya ce ambaliyar ta kuma katya hanyoyin da suka haɗa ƙananan hukumomin biyu da al’umma da kuma wasu sassan jihar a wurare 6 a kan babbar hanyar.

Ya kara cewar, hanyoyin da za abi don kawo agajin gaggawa, ga al ummar da abin ya shafa, sune jama a na buƙatar kwale-kwale 14 a matsayin hanyar sufuri don ketare hanyoyin da suka yanke don ci gaba da kasuwancinsu na yau da kullum,” in ji shi.

Alfijr Labarai

Kabir ya shawarci al’ummomin da suyi kaura zuwa wuraren da babu ambaliyar domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

A masa bangaren Gwamna Bala ya jajanta wa al’ummar yankin kan mutuwar mutane uku da lalata gidaje da gonaki a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.

Daga karshr ya yi kira da a haɗa karfi da karfe wajen magance munanan illolin da ambaliyar ruwa ta addabi al’umma a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *