Rikici Ya Barke A Majalisar Wakilai Kan Buƙatar Lalle Sai An Gayyaci Shugaba Tinubu

IMG 145816 08726 1783519107794

An samu wata taƙaddama da cece-kuce a Majalisar Wakilan Tarayya a yau ranar Laraba bayan wasu ‘yan majalisar sun yi sabani kan wani ƙuduri da ke neman a gayyaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin ya yi bayani kan wasu batutuwa da suka shafi kuɗaɗen gwamnati.

Hatsaniyar ta fara ne a yayin zaman majalisar lokacin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Okpe/Sapele/Uvwie ta jihar Delta, Benedict Etanabene, ya tashi da batun gaggawa (Point of Privilege). ‎

Etanabene ya jawo hankalin majalisar zuwa wata takarda da Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya fitar a ranar 29 ga Yuni, wadda ta shafi wasu muhimman batutuwan gudanar da kuɗaɗen gwamnati.

Sai dai yayin da aka fara tattaunawa kan buƙatar gayyatar Shugaba Tinubu, wasu ‘yan majalisar sun nuna adawa da hakan, yayin da wasu kuma suka goyi bayan a ci gaba da tattaunawa.

Wannan ya janyo hayaniya da cacar baki a zauren majalisar, lamarin da ya sa aka ɗan dakatar da zaman na wani lokaci kafin a ci gaba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a cimma matsaya ta ƙarshe kan ko za a gayyaci Shugaba Tinubu ko a’a ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *