Bankada! Asirin mutumin da ake zargi da ƙirƙirar hukumar gwamnati ta bogi, tare da karɓar fiye da biliyan 1.3 a matsayin kasafin kuɗi ya tonu

IMG 20260701 WA1179

Aminu Bala Madobi.

Rahotannin da Jaridar Alfijir Labarai ta bankado sun bayyana cewa wani mutum mai suna Prince Adeniyi Matthew ana zarginsa da ƙirƙirar wata hukumar gwamnati ta bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council, inda ya naɗa kansa da kansa a matsayin Darakta Janar (DG) na hukumar.

Lamarin ya jawo cece-kuce da mamaki, kasancewar ana zargin ya gudanar da ayyuka na hukuma tsawon lokaci ba tare da an gano cewa hukumar ba ta da sahihancin doka ba.

A cewar rahotannin, bayan kafa hukumar, mutumin ya samu ofis a harabar sakatariyar Gwamnatin Tarayya, abin da ya sa mutane da dama suka ɗauka cewa hukuma ce ta gaskiya. Haka kuma, ya buɗe asusunp banki a Babban Bankin Najeriya (CBN) da sunan hukumar, lamarin da ya ba ta damar gudanar da mu’amaloli kamar kowacce hukuma ta gwamnati.

Rahotannin sun ƙara da cewa abin mamakin shi ne yadda aka ware wa hukumar kuɗaɗen da suka kai Naira biliyan 1.302 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Wannan ya sa ake ta tambayar yadda wata hukuma da ake zargin ba ta da tushe ta samu shiga cikin tsarin kasafin kuɗin ƙasa.

Baya ga hakan, ana zargin Prince Adeniyi Matthew ya riƙa gayyatar jakadun ƙasashen waje zuwa tarurruka, inda yake tattauna batutuwan da suka shafi hulɗar ƙasa da ƙasa. Haka kuma, ya gudanar da zaman tattaunawa da wasu ministoci kan batutuwan da ake kira na dabarun gwamnati, abin da ya ƙara tabbatar da yadda ake kallon hukumar a matsayin halastacciya.

Rahotannin sun kuma bayyana cewa mutumin ya wakilci Najeriya a wasu tarurrukan ƙasa da ƙasa, inda ake zargin ya gabatar da kansa a matsayin shugaban wannan hukuma. Wannan ya tayar da hankulan jama’a, musamman ganin irin matsayin da ake zargin ya samu a idon jami’an gwamnati da na ƙasashen waje.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da cikakken bayani kan yadda aka bari wannan lamari ya faru ba. Ana sa ran za a gudanar da cikakken bincike domin gano yadda aka ƙirƙiri hukumar, yadda ta samu amincewa a wasu matakai, da kuma yadda aka sanya mata kuɗaɗe a kasafin kuɗin ƙasa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *