Jami’an hukumar DSS sun kama tsohon Minista Uche Nnaji

IMG 234654 01726 1782946020354

Jami’an Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) sun kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a safiyar yau Laraba a filin jirgin sama na Akanu Ibiam  da ke Enugu.

An kama tsohon ministan ne yayin da ya ke shirin hawa wani jirgin sama mai zaman kansa zuwa Abuja.

Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun ce an kama Nnaji, wanda ya yi murabus daga mukaminsa a watan Oktoban da ya gabata bayan wata cece-kuce, bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) kan zargin yin jabun takardun shaida.

Daga baya DSS ta miƙa shi ga hukumar yaƙi da cin hancin.

A cewar majiyoyin, ICPC ta sha gayyatar tsohon ministan bayan samun koke-koke kan yadda ya gudanar da harkokin ma’aikatarsa, don haka ta nemi taimakon DSS wajen kama shi.

Nnaji ya yi murabus daga matsayin minista a ranar 7 ga Oktoba, 2025, bayan wata yar hatsaniya da ta shafi takardun shaidarsa daga Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da kuma Hukumar NYSC.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *