Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa tsarin tantance bayanan ’yan ƙasa na Hukumar NIMC ya taimaka wajen cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajjin 2026.
Jaridar Punch ta rawaito ministan ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar NIMC ta 2026.
A cewarsa, an kama mutanen ne a filin jirgin saman Katsina a ranar Alhamis bayan sun dawo daga Makka, sannan aka miƙa su ga Hukumar Tsaro ta DSS domin ci gaba da bincike.
Tunji-Ojo ya ce an samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne saboda haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya tare da alaƙarsu da tsarin bayanan Interpol.
Ya bayyana cewa sabuwar dokar NIMC za ta ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar haɗa bayanan hukumomi daban-daban, tare da taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanai da sauran laifukan tsaro.
Ministan ya ƙara da cewa a baya tsarin bayanan ’yan ƙasa a Najeriya ya kasance a rarrabe, amma yanzu ba za a iya samun fasfo na Najeriya ba tare da amfani da bayanan NIMC ba.
Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar NIMC ta 2026 a gaban shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu manyan jami’an gwamnati.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t