Abin takaici ne a ce gwamnati ta kasa maganin matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya shekaru 20 –  In Ji Umar Ajiya

FB IMG 1781037599142

Daya daga cikin dattijan ƙasa, Umar Ajiya, ya nuna damuwa kan karuwar matsalolin rashin tsaro, garkuwa da mutane, satar shanu da fashi da makami a Najeriya, yana mai gargadin cewa lamarin na iya rikidewa zuwa babbar matsala idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ajiya ya ce Nijeriya ta kwashe kusan shekaru 20 tana fama da matsalolin tsaro daban-daban kuma an kasa shawo kan lamarin.

Ya bukaci gwamnati ta kara samar da kudade ga hukumomin tsaro, ta inganta amfani da fasahar zamani kamar jiragen marasa matuka, tare da karfafa tattara bayanan sirri da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Ajiya ya kuma ba da shawarar kafa ’yansandan jihohi, tabbatar da rajistar dukkan ’yan kasa ta hanyar NIN, da kuma daukar matakan dakile garkuwa da mutane da satar shanu.

Ya jaddada cewa tsaron kasa nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati da al’umma baki daya, yana mai cewa hadin kai da amfani da fasaha za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya a kasar.

Ajiya ya ƙara da cewa duk da kokarin da gwamnati ke yi, ba za a iya shawo kan matsalar tsaro ba sai da hadin kan al’umma ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri da tallafawa jami’an tsaro.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *