Ofishin jakadancin ƙasar Russia a Najeriya ya musanta hannu a cikin amfani da tutar kasar da wasu masu zanga-zanga ke yi.
Alfijir labarai ta ruwaito qasu masu zanga-zanga na daga tutar ƙasar Russia a yayin zanga zangar a kwanakin nan a jihar da sauran wasu jihohin.
Dama can an zargi ƙasar Rashan da hannu dumu-dumi a rikicin siyasa da ya shafi kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso.
Wanda hakan ya haifar da damuwa kan shigar wata kasa daga ketare kan al’amuran da suka shafi cikin gida.
Sai dai a sanarwar da ofishin jakadancin Russia a Najeriya ya fitar ya ce kasar bata shiga al’amuran da suka shafi wata kasa ciki har da Najeriya ba, kuma abinda masu zanga zangar suke yi ya saba da manufofin Russia.
Sanarwar ta kuma ce ƙasar Russia na girmama dimukordiyyar Najeriya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj